Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Kongo DRC ce tafi yawan mutanen da suka kauracewa muhallansu a Afrika
2019-12-22 16:46:20        cri
Sama da mutane miliyan 5 ne suka kauracewa gidajensu a jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC), hakan ya nuna cewa, itace kasar da tafi yawan mutanen da suka kauracewa muhallansu a Afrika baki daya, inji MDD.

Galibin mutanen da lamarin ya shafa sun kauracewa gidajensu ne sakamakon matsalolin tashe tashen hankula, a halin yanzu akwai 'yan gudun hijira kusan 517,000 dake neman mafaka a kasar wadanda suka tsallaka daga makwabtan kasashe, kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya bayyana hakan a ranar Juma'a.

Bugu da kari, DRC tana cigaba da fuskantar tarin matsalolin karancin kayayyakin tallafin jin kai, wadanda ake bukatar amfani dasu nan da wasu 'yan watanni masu zuwa, yayi gargadin cewa, ana bukatar kudaden gudanar da tallafin masu yawan gaske.

A bisa ga alkaluman da ofishin ayyukan jin kai na MDD ya fitar, kusan mutane miliyan 16 a DRC ne suke cikin tsananin matsalar karancin abinci a shekarar 2019, kuma wannan matsalar cututtuka masu yaduwa ma ta shafi rayuwar miliyoyin mutanen kasar.

Duk da karancin kudaden gudanarwar da aka fuskanta a wannan shekara, MDD da hukumomin bada agaji sun samar da taimakon abinci ga mutane sama da miliyan 4, kana an samar da tallafin kiwon lafiya ga sama da mutane miliyan 2.5, haka zalika MDDr ta raba taimakon kudaden da ya zarta dalar Amurka miliyan 20, inji kakakin MDD.

A cewarsa, a shekarar 2020, MDD zata ninka kokarinta wajen kai dauki ga mabukatan, kuma a halin yanzu hukumar tana neman kimanin dala biliyan 1.8 domin taimakawa mutane kusan miliyan 8.1 a DRC.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China