Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An ceci dabbobin 12 baki daya daga hadarin amon wuta
2019-12-28 14:26:37        cri

 

 

 

Yadda aka rika samun amon wuta da duwatsu a kwanakin baya a kasar Australia, ya sa dabbobin Koala da dama dake fuskantar barazanar bacewa daga doron kasa rasa wurin zama.A yankin Blue Mountains da ke kasar, kungiya mai ceton dabbobin Koala, ta ceci dabbobin 12 baki daya, maza uku, mata biyar, har ma da jariri 4. An ce, a zamanin da, akwai Koala kimanin miliyan 400 a doron duniya, amma yanzu dubu 300 ne kawai suka rage, don haka ceton su na da matukar muhimmanci.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China