Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#MacaoSAR 20#Yankin Macao na ci gaba da karfafa tsarin "kasa daya amma tsarin mulki biyu", in ji Xi Jinping
2019-12-20 11:10:42        cri
Yau Jumma'a, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, nasarar da yankin Macao ya samu game da aiwatar da tsarin "kasa daya amma tsarin mulki biyu" ta nuna cewa, mazauna yankin suna iya daukar nauyin da ke kansu a cikin wannan sabon zamanin da ake ciki. Suna tuna bukatunsu da ma moriyar yankin Macao, da moriyar kasar Sin baki daya. Sun kuma dora muhimmanci kan ayyukan aiwatar da tsarin "kasa daya amma tsarin mulki biyu" da yadda "al'ummar Macao za su gudanar da harkokin Macao cikin 'yanci", sa'an nan kuma, su hada burinsu da babban burin farfado da al'ummar Sin baki daya waje guda. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China