Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bawa yara masu fama da talauci kayan inganta rayuwa da karatu a Togo
2019-12-19 16:09:26        cri
Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Togo, gami da kungiyar sada zumunta ta Sinawa mazauna Togo sun baiwa Togo kyautar wasu kayayyaki jiya Laraba, domin taimakawa yara kanana masu fama da talauci inganta harkokinsu na rayuwa da na karatu.

Ministar inganta rayuwar al'umma da hakkokin mata ta Togo ta bayyana cewa, kayan da kasar Sin ta bayar za su taimakawa yara sama da dubu shida wadanda ke fama da matsalar rayuwa, al'amarin da ya shaida irin dadadden zumunci tsakanin kasashen biyu.

Shi ma a nasa bangaren, jakadan kasar Sin dake Togo Chao Weidong ya ce, Sinawa mazauna Togo da 'yan asalin kasar sun dade da kulla zumunci da hada gwiwa a tsakaninsu, kuma Sin na fatan ci gaba da karfafa hadin-gwiwa tare da Togo a fannin raya tattalin arziki da tallafawa mutanen dake fama da talauci.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China