Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar makwabtan Macau na kokarin samar da hidima ga al'umma, "Kwamitin unguwa" mafi girma a zuciyar mazauna yankin
2019-12-19 14:59:38        cri

A gabannin bikin tsofaffi na gargajiyar kasar Sin na bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasika ga ma'aikata masu aikin sa kai na cibiyar Yijun ta kungiyar makwabta ta yankin Macau, don gaida su da kwarfafa musu gwiwa, hakan ya jawo hankula sosai a yankin, a waje guda kuma, an soma mayar da hankali sosai kan wannan kungiya.

 

An kafa kungiyar makwabta ta Macau ne a shekarar 1983, a cikin shekaru 20 da suka wuce tun bayan da aka dawo da Macau karkashin ikon kasar Sin, kungiyar ta rika shiga ayyukan taimakawa al'umma, da mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi zaman rayuwar jama'a, sannu a hankali ta bullo da wani tsarin ba da hidima dake shafar daukacin al'ummar yankin Macau, matakin da ya saukaka al'amura ga jama'ar yankin, hakan ya sa kungiyar ta kasance "Kwamitin unguwa" mafi girma da tasiri a zukatan mazauna yankin. Ya zuwa yanzu, kungiyar ta kafa makarantu guda biyu,da gidajen renon kananan yara guda 3, da cibiyoyin ba da hidima iri daban daban sama da 30 da dai sauransu, ma'aikatan kungiyar kuma sun karu daga 2 zuwa 700.

Cibiyar Yijun wadda ta samu wasika daga shugaba Xi Jinping, wata hukuma ce dake ba da hidima ga tsofaffi karkashin shugabancin kungiyar makwabta ta Macau. Chen Yulian, mai shekaru 75 a duniya ta gayawa wakilinmu cewa, ko da yake yau shekaru 10 ke nan, amma ba ta taba mantawa da yadda shugaba Xi Jinping ya kai musu ziyara a yayin da yake rangadin aiki a Macau a shekarar 2009 ba. Ta ce,

"Babu shakka ba zan manta da yadda ake ciki a lokacin ba, shugaba Xi ya zo cibiyarmu don ya gaishe mu, mu ma mun ba shi wani kayan da muka yi da hannu. Shugaba ya tambaye mu yaya zaman rayuwarmu bayan dawowar yankin karkashin ikon kasar Sin, mun ba shi amsa cewa, muna jin dadin zaman rayuwa sosai, an ba mu hidimar jinya kyauta, da kudin ritaya ko fansho, muna jin dadi sosai."

Kamar yadda Chen Yulian ta fada, tun bayan dawowar Macau karkashin ikon kasar sin, zaman rayuwar mazauna yankin na kara samun kyautatuwa. Ma Teng, wadda take aikin sa kai a cibiyar Yijun ta bayyana cewa, gwamnatin yankin Macau ta bullo da wani cikakken tsarin kula da tsoffi, tsoffi za su iya ganin likita kyauta, kuma ana ba su kudin ritaya na watanni goma sha uku a ko wace shekara, baya ga haka, gwamnatin tana ba da tallafin kudi ga kungiyoyin al'umma don su gudanar da ayyukan kula da tsofaffi, a cewar Ma Teng,

"Yankin Macau ya samu gyaran fuska sosai a cikin wadannan shekaru 10, tsoffi suna jin dadin zama sosai. Da kasarmu ta ci gaba, yankin Macau ya ci gaba, haka kuma da kasarmu ta yi karfi, Macau ma ya kara karfi."

A cikin wasikar da shugaba Xi Jinping ya aike wa tsofaffi na Macau, ya bayyana fatansa na ganin, tsofaffin dake aiki a cibiyar Yijun za su kara baiwa matasan Macau labarai game da yadda yankin yake kafin dawowarsa da bayan dawowarsa karkashin ikon kasar Sin, don kara musu kwarin kwiwa wajen yada tunanin kishin kasa da kaunar Macau, kana da sa himma wajen shiga ayyukan raya yankunan Guangdong-HK-Macau, don gina yankin Macau da kara inganta shi. Game da haka, kungiyar makwabta ta Macau ta riga ta soma aikinta a wannan fannin. Bisa ayyukan raya yankunan Guangdong-HK-Macau, yankunan uku na kara yin cudanya da juna da ba a taba ganin irinsa ba a da, kungiyar makwabta ta Macau ta soma fadada hidimomin da take samarwa daga mazauna yankin Macau zuwa dukkan yankunan uku. A watan da ya wuce, kungiyar ta kafa wata cibiyar ba da hidima a Hengqin na Guangdong, wadda ta kasance wani cikakken aikin da ba hidima ga al'umma na farko da kungiyar Macau ta kaddamar a babban yankin kasar Sin, inda aka yada fasahohin ba da hidima ga al'umma da Macau ya samu zuwa ga babban yankin kasar, ta yadda ake iya samar da hidima ga jama'a da dama a yankunan uku. Daraktan ofishin kula da harkokin waje na kungiyar makwabta ta Macau, Tian Yi ya bayyana cewa,

"Yankin Macau ya dade yana raya ayyukan ba da hidima ga al'umma, don haka ya samu kwarewa da dabaru a wannan fannin, musamman ma ga wasu rukunin mutane na musamman, ciki har da tsofaffi, da tsofaffi dake zaune su kadai, da wasu kananan yara, musamman ma 'yan kasa da shekaru 3."

Ke Wen 'yar yankin Macau wadda ke zama a Hengqin ta bayyana cewa, tana iya samun hidimar al'umma kamar yadda ta samu a Macau.

"A nan ma akwai masu aikin sa kai, akwai wasanni da filayen wasanni, dakunan karatu da dai sauransu, ana samar da hidima a dukkan fannoni."(Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China