Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Farin-dango na yaduwa a yankin kahon Afirka
2019-12-19 09:34:42        cri

Hukumar abinci da aikin gona ta MDD (FAO) ta yi gargadin cewa, farin-dango masu hadarin gaske ga amfanin gona na yaduwa a sassan kahon Afirka, a daidai gabar da farin ke ci gaba da hayayyafa a gabashin kasar Habasha da wasu sassa dake daura da Somaliya.

Da take karin haske cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar FAO ta ce, duk da feshin maganin farin da ke gudana a yankin Somali a gabashin kasar Habasha, ana sa ran wasu sabbin tsutsotsi za su fara yin gungu a Ogaden a karshen wannan wata, lamarin da aka iya yin barazana ga amfanin gona.

FAO ta ce, da alamun wasu daga tsutsotsin sun doshi kudu zuwa arewa maso gabashin Kenya da kuma daura da yankunan kudancin Somaliya. Sanarwar na kira ga hukumomi da su hada karfi da karfe don yin safiyo a kai a kai, da bayar da bayanai a kan lokaci da daukar managartan matakan kariya don daga matsayin wadannan ayyuka a cikin makonni da ma watanni dake tafe.

Bugu da kari, hukumar ta lura cewa, farin-dangon na ci gaba da hayayyafa a dukkan sassan tekun bahar maliya,inda tsutsotsi da dama suka taru a gabar yammacin Yemen, baya ga wasu sabbi da aka haifa.

A cewar FAO, a kasar Sudan ma, an yi feshin magani ta sama da kasa a sama da eka 12,000 na filin noma a kwanaki sha biyar na farko na watan Disamba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China