Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta baiwa Namibiya tallafin abinci
2019-12-18 10:55:16        cri

Jiya Talata ne, kasar Sin ta hannun shirin samar da abinci na duniya (WFP) ta mikawa yankin yammacin yankin Kavango dake arewacin kasar Namibiya da bala'in fari ya shafa tallafin gaggawa na tan 1,300 na kayan abinci, wanda ake saran mutane 77,400 za su amfana da shi, galibi mata da kananan yara masu rauni.

Da yake jawabi yayin bikin mika kayayyakin da ya gudana a Nkurenkuru, babban birnin yankin, jakadan kasar Sin dake Namibiya, Zhang Yiming, ya ce kasar Sin ta samar da taimakon kayan abinci da darajarsu ta kai dala miliyan 1 ne karkashin asusun hadin gwiwar kasashe masu tasowa, wanda shirin WFP ya aiwatar.

Jakada Zhang ya ce, yana sane cewa, shirin tallafin da kasar Namibiya ta kaddamar, zai samar da kaso 14 cikin 100 na abinci mai gina jiki da kowane mutum ke bukata a rana, kuma aiwatar da wannan shiri zai kara adadin zuwa kaso 60 cikin 100.

A jawabinta yayin bude bikin, Kansila mai wakiltar mazabar Nkurenkuru, Damian Nakambare, ta bayyana gudummawar kayayyakin da suka hada da garin masara da man girki da gishiri, za su taimakawa magidantan da bala'in ya fi shafi a yankin.

Ta ce, wannan shi ne gudummawa na uku da kasar Sin ta samar, tun lokacin da shugaban kasar ta Namibiya ya ayyana bala'in farin.

Da yake jawanbi, darektan shirin samar da abinci na duniya dake Namibiya (WFP) Bai-Mankay Sankoh, ya bayyana cewa, kasar Sin ta sha tallafawa WFP a yakin da take yi da yunwa, tana kuma kan gaba cikin kasashen dake ba da agaji a yankin kudancin Afirka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China