Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin tsara kundin tsarin mulkin Aljeriya ya tabbatar da sakamakon babban zaben kasar
2019-12-17 11:20:07        cri

Kwamitin tsara kundin tsarin mulkin kasar Aljeriya ya tabbatar da sakamakon babban zaben kasar wanda ya gudana a kwanakin baya, inda ya ayyana, Abdelmadjid Tebboune a matsayin sabon shugaban kasar.

Shugaban kwamitin Kamel Fenniche ya sanar da cewa, Abdelmadjid Tebboune ya samu kuri'un da yawansu ya kai kaso 58.13, kuma bisa dokar zaben Aljeriya, shi ne sabon shugaban kasar. Fenniche ya ce, za'a gudanar da bikin rantsar da shi a wannan mako.

Abdelmadjid Tebboune, mai shekaru 74 a duniya, ya taba zama firaminista da minista har ma da mukamin gwamna a kasar ta Aljeriya.

A ranar 2 ga watan Afrilun bana ne, tsohon shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya yi murabus, amma an dakatar da babban zaben kasar har sau biyu wanda aka shirya gudanarwa a watan Afrilun. Kana a ranar 15 ga wata Satumba, shugaban kasar na wucin gadi Bensalah ya sanar da gudanar da babban zaben kasar a ranar 12 ga watan Disamba.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China