Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci nahiyar Afirka da ta inganta tsare-tsarenta don cimma nasarar manufofin ci gaba
2019-12-17 10:35:25        cri

MDD ta bukaci kasashen nahiyar Afirka, da su inganta tsare-tsarensu, ta yadda za su cimma nasarar manufofinsu na raya kasa.

Babban jami'in ba da shawara na shiyya kan raya kasa a hukumar MDD mai kula da harkokin tattalin arziki Afirka (UNECA) Sylvain Boko, ya shaidawa wani dandali a Nairobin Kenya cewa, akwai bukatar kasashen nahiyar ta Afirka, su bullo tare da karfafa hanyoyinsu na kididdiga da raya kasa, a matsayin wata kafa ta karfafa yin abubuwa a bayyane, da sarrafa kudade, ta yadda zai dace da manufofin raya kasa.

Boko ya ce, nasarar shirye-shireyn raya kasa, ta dogara ne kan isassun muhimman bayanan da ake bukata, da suka hada da muhimman alkaluman kididdiga da suka shafi ci gaban tattalin arziki, talauci da haraji, da cinikayya da haihuwa da mace-mace. A karshe, abin da ya rage shi ne, yadda za a tsara da ma aiwatar da matakan raya kasa, wadanda za su taimaka wajen farfado da tattalin arziki da kuma dorewar matakan.

Jami'in yana magana ne, yayin taron karawa juna sani na kasa da kasa game da kara karfin gwamnatocin Afirka na sarrafa kudade a fannin raya kasa. Yana mai cewa, a cikin shekaru 20 din da suka gabata, shirin raya kasa ya samu karbuwa a nahiyar ta Afirka.

Kasar Kenya, na daga cikin kasashen Afirka biyar da aka zaba don gwada shirin samun horon.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China