Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Qishan:Kamata ya yi a zurfafa fahimtar juna tsakanin jama'ar Sin da al'ummar duniya
2019-12-16 20:13:19        cri

Yau Litinin, mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan, ya gana da wasu tsoffin jami'an kasa da kasa, da wakilan tsoffin jakadun kasashen waje dake Sin, ciki hadda tsohon firaministan kasar Japan Yukio Hatoyama, wadanda suka halarci bikin tayar murnar cika shekaru 70 da kafuwar kungiyar jama'a mai kula da harkokin diplomasiyya ta kasar Sin a nan birnin Beijing.

Yayin ganawar tasu, Wang Qishan ya nanata cewa, kamata ya yi a zurfafa fahimtar juna tsakanin jama'ar kasar Sin da al'umomin kasashen duniya, da ingiza tuntubar juna, da tattaunawa da juna, da hadin kan kasa da kasa, don ba da gudunmawa ga zaman lafiya da lumana, da kuma wadata a duniya.

A nasa bangare, Yukio Hatoyama da sauran mahalarta taron, sun bayyana niyyarsu, ta sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar kasashensu da kasar Sin, da kara taka rawa wajen ingiza zumunci tsakanin jama'ar bangarorin biyu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China