Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 30 sun rasu sakamakon rubzawar mahakar zinariya a Congo-Kinshasa
2019-12-16 15:24:08        cri
Jiya Lahadi, wani jami'in kasar Congo-kinshasa ya sanar da cewa, a kalla mutane 30 sun rasu sakamakon rubzawar wata mahakar zinariya a lardin Haut-Uele dake arewa maso gabashin kasar.

Wani jami'in lardin Haut-Uele ya ce, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi kwanan baya, ya haddasa rubzawar wata mahakar zinariya a ranar 13 ga wata, lamarin da ya yi sanadiyar kasa ta binne wasu ma'aikatan da suke aiki a cikin mahakar a lokacin. Ya zuwa ranar 15 ga wata, masu aikin ceto sun gano gawawaki guda 30, kuma mai yiyuwa ne wannan adadi zai karu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China