Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron ministocin tsaro na kasashen Afrika a Masar
2019-12-16 09:44:55        cri

Jiya Lahadi aka bude taron kwamitin ministocin tsaro game da batutuwan da suka shafi zaman lafiya da tsaro na kasashen Afrika a sabuwar fadar mulki kasar Masar.

Kwamitin ministocin, daya ne daga cikin hukumomin kungiyar tarayyar Afrika, wanda aka dorawa alhakin kula da al'amurran tsaro a matakin farko na nahiyar da kuma aiwatar da shirin hadin gwiwa na manufofin wanzar da tsaro da zaman lafiyar Afrika.

Kwamitin har ila yau shi ne ke lura da ayyukan 'yan sanda, da cibiyoyin nazarin al'amurran tsaro da tattara bayanan sirri na kungiyar tarayyar Afrika a fannonin haramta amfani da makamai da yaki da ta'addanci.

Taron na kwanaki biyar zai samu halartar kwararru, shugabannin hukumomin tsaro da kuma ministocin tsaro.(Ahmd Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China