Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in MDD: Sin ta nuna bajinta wajen cimma nasarar samar da abinci
2019-12-16 09:26:37        cri

Qu Dongyu, darakta janar na hukumar samar da abinci ta MDD (FAO), ya ce kasar Sin ta nuna bajinta wajen cimma nasarar samar da abinci.

A lokacin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a taron dandalin matasa na kasa da kasa dake gudana a birnin Sharm El Sheikh na kasar Masar, Qu ya ce, kasar Sin ta samar da abinci ga kashi 22 bisa 100 na yawan al'ummar duniya ta hanyar amfani da kashi 7 bisa 100 na filayen noma masu inganci.

Ya ce, samar da ingantaccen tsarin gudanar da aikin gona, da amfani da fasahohin zamani, gami da shugabanci nagari suvne muhimman dalilan da suka baiwa kasar manyan nasarorin bunkasa aikin gona.

Ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da wasu kyawawan manufofi da nufin janyo masu zuba jari a fannin aikin gona daga bangarorin gwamnati da masu zaman kansu, inda suka hada hannu wajen janyo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje.

Babban jami'in na FAO ya ce, kasar Sin tana ci gaba da yin musayar irin nasarorin da ta samu a fannin aikin gona tare da kawayenta kasashen Afrika cikin gomman shekaru, kuma a shirye take ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwar a bangaren amfani da sabbin dabarun zamani, da sabbin irin shukawa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China