Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Masar ya yi kira da a hada hannu don yaki ta'addanci
2019-12-16 09:18:02        cri

Shugaban kasar Masar Abdul Fattah al-Sisi, ya yi kira ga kasashen duniya da su hada karfi da karfe wajen ganin an yaki ayyukan ta'addanci. Al-Sisi, ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi a taron dandalin matasa na kasa da kasa karo na uku da aka bude ranar Asabar din da ta gabata a birnin yawon shakatawa na Sharm El Sheikh dake bakin ruwa a kasar ta Masar.

Da yake tsokaci yayin zaman tattauna kalubalen dake addabar zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, shugaban ya bayyana cewa, kungiyoyin 'yan ta'adda na iya yin illa ga babbar kasa yayin da aikin ta'addanci daya ko biyu na iya lalata harkokin yawon bude ido baki daya.

Ya jaddada cewa, yaki da ta'addanci yana bukatar kaimi da ma hadin gwiwar kasa da kasa, ko da ayyukan ta'addanci ba su yi tasiri kai tsaye a wasu kasashe ba.

Bugu da kari, shugaban ya bayyana cewa, wajibi ne a dauki kwararan matakai kan kasashen dake goyo baya da ma amfani da batun ta'addanci don cimma manufofinsu.

Ya ce, idan har ba a dauki matakin da ya dace kan irin wadannan kasashe ba, hakika ayyukan ta'addanci za su karu a shiyyar da nahiyar Afirka, kana duniya za ta shiga wani irin hali mai tsanani.

A shekarar 2017 ne aka kaddamar da taron dandalin matasa na kasa da kasa. Taron dandalin na bana na kwanaki hudu, wanda ya hallara dubban matasa daga sama da kasashe 100, ya tattauna kan batutuwan da suka hada da juyin juya halin masama'antu, da tsaron abinci da kalubalen da muhalli ke fuskanta da kuma kwaikwayon tunanin dan-Adam.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China