Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Libya masu sansani a gabashi sun kaddamar da harin karshe na neman karbe ikon babban birnin kasar
2019-12-13 11:19:53        cri
Khalifa Haftar, kwamandan sojojin Libya masu sansani a gabashin kasar, ya ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar karshe ta kaddamar da harin sojoji a yankin birnin Tripoli da kewaye.

Haftar ya fada cikin wani jawabi ta tashar talabijin ta Libya Al-Hadath cewa, "A yau, mun kaddamar da farmakin karshe na yakin da muke yi da nufin kutsawa ainihin kwaryar babban birnin kasar".

Khalifa Haftar, shine ke jagorantar rundunar sojojin Libya masu sansani a gabashin kasar yana jagorantar kaddamar da hare haren soji a yankunan birnin Tripoli da kewayensa tun a farkon watan Afrilu, a kokarin da suke na neman kwace ikon babban birnin kasar da hambarar da gwamnatin kasar dake samun goyon bayan MDD.

Dubban mutane aka hallaka a sanadiyyar fadan, wasu mutanen sama da 120,000 sun tsere daga gidajensu a sakamakon rikicin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China