Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban aikin canja alakar ruwa na Sin ya tura cubic mita biliyan 30 na ruwa
2019-12-12 19:45:53        cri

Ma'aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin shekarun biyar da suka gabata, an tura a kalla cubic mita biliyan 30 na ruwa karkashin babban aikin canja akalar ruwa na kasar.

Rahotanni na cewa, sama da mutane miliyan 120 ne suka ci gajiyar kashin farko na aikin canja akalar ruwan daga kudu zuwa yankin arewacin kasar.

An yi kiyasin cewa, ko wane mutum a kasar, yana samun kaso 28 cikin dari na matsakaicin albarkatun ruwa a duniya, kana akwai gibi kan yadda ake raba albarkatu ruwa a sassan kasar. Bayanai na nuna cewa, Allah ya albarkaci kudancin kasar da ruwa sabanin arewacin kasar, lamarin da ya sanya tilas a gudanar da aikin tura ruwa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China