Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: A yi hadin gwiwa don tinkarar sauyin yanayin duniya
2019-12-12 14:54:33        cri

yanayin duniya da ke gudana a Madrid na kasar Sifaniya, shugaban tawagar kasar Sin, kana mataimakin minista mai kula da harkokin muhalli na kasar, mista Zhao Yingmin, ya furta a jiya Laraba cewa, ya kamata bangarori daban daban su yi hadin gwiwa wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi.

A jiya Laraba, an yi wani taro na manyan shugabanni karkashin taron nan na tinkarar sauyin yanayi, inda mista Zhao Yingmin ya ce, matsalar ta shafi makomar daukacin bil Adama, don haka akwai butakar dukkan kasashen duniya su hada hannu a kokarin tinkarar batun. A cewar jami'in, yarjejeniyar Paris da ta tanadi ayyukan da za a yi a kokarin daidaita matsalar sauyin yanayi bayan shekarar 2020, wata babbar nasara ce da aka samu ta hanyar hadin kan bangarori daban daban, don haka kasar Sin na fatan ganin za a aiwatar da yarjejeniyar, tare da kare tsarin kasancewar bangarori daban daban a duniya. Shugaban na tawagar kasar Sin ya ce,

"Abin da ya fi muhimmanci, shi ne a yi kokarin fahimtar burikan da aka sanya cikin yarjejeniyar Paris, da manufar daukar nauyi na bai daya, ba tare da nuna bambanci ba, sa'an nan a kara kokarin aiwatar da yarjejeniyar. Ya kamata mu ki yarda da mataki na kashin kai, da kuma ra'ayin kariyar ciniki, don tallafawa kokarin tinkarar sauyin yanayi a duniya."

A ganin kasar Sin, dalilin da ya sa a samu koma baya ga aikin tinkarar sauyin yanayi a duniya shi ne, an kasa aiwatar da shirin da aka tsara game da matakan da za a dauka kafin shekarar 2020. Mista Zhao ya ce, ya kamata a mai da hankali kan matakan da kasashe masu sukuni suka dauka, da kuma yadda suka kasa cika alkawuran da suka dauka a kokarin aiwatar da shirin ayyukan da za a yi kafin shekarar 2020, wajen taro na wannan karo. Ya ce,

"Ya kamata bangarorin da ke halartar taron na wannan karo su yi nazari kan ayyukan da aka yi kafin shekarar 2020, sa'an nan su duba gibin da aka samu kan ayyukan da kasashe masu sukuni suka yi, masamman ma a fannonin rage fitar da iska mai dumama yanayi, da samar da tallafi. Ta yadda za a shirya wasu matakai na neman cike wannan gibi, don magance kara dora wa kasashe masu tasowa nauyi, ta hanyar sabon shirin ayyukan da za a tsara na bayan shekarar 2020. Har ila yau, muna kira ga bangarori daban daban na duniyarmu da su hada kansu, don neman kaddamar da 'Gyararriyar dokar Doha ta yarjejeniyar Kyoto' tun da wuri."

Ban da haka, jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, a shekarar 2020 za a fara aiwatar da yarjejeniyar Paris, amma matsalar rashin samar da isasshen tallafi ga kasashe masu tasowa, na kara shiga wani yanayi mai tsanani. Saboda haka, a cewar jami'in, kamata ya yi tallafin da kasashe masu sukuni suke samarwa ya dace da matakai masu yakini da kasashe masu tasowa suke dauka. Mista Zhao ya yi kira ga kasashe masu karfin tattalin arziki da su dauki wasu hakikanann matakai, don cika alkawarin da suka yi na samar da dalar Amurka biliyan 100 ga kasashe masu bukata a kowace shekara, don taimaka musu tinkarar sauyin yanayi. Sa'an nan su kara samar da wasu kudade na tallafawa ayyukan jama'a, tare da yin amfani da wadannan kudade ba tare da rufa-rufa ba.

A karshen jawabinsa, mista Zhao Yingmin, shugaban tawagar kasar Sin, kana mataimakin ministan kare muhalli na kasar, ya ce ko da yake kasar Sin na fuskantar matsalar neman ci gaban tattalin arziki, amma za ta cika alkawarin da ta dauka game da tinkarar matsalar sauyawar yanayi. Mista Zhao ya ce,

"Kasar Sin wata babbar kasa ce dake kan hanyar tasowa, inda ake fama da matsalolin rashin daidaito a fannin raya kasa, da gaza samun cikakken ci gaba a wasu fannoni. Duk da haka, kasar Sin ba ta taba yin kasala ba, a kokarin daukar matakai don tinkarar sauyin yanayi."

A cewar jami'in, kasar Sin za ta tsaya kan manufarta ta kokarin taka rawar gani a fannin tinkarar sauyawar yanayi, da neman cika dukkan alkawuran da ta dauka, tare da samar da gudunmowa, ga yunkurin samar da kyakkyawar makoma ga daukacin bil'adama ta bai daya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China