Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A kalla mutane 70 sun rasu sakamakon harin da aka kai a wani sansanin sojan Nijar
2019-12-12 10:55:06        cri
Rahotanni daga rundunar tsaron Jamhuriyar Nijar, sun ce a daren ranar 10 ga wata, wasu masu dauke da makamai da ba'a san ko su wanene ba sun kai hari a wani sansanin soja dake yammacin kasar, lamarin da ya haddasa rasuwar sojoji a kalla 70, kana a halin yanzu, akwai mutane sama da 10 da ba a san inda suke ba.

Wani jami'in rundunar ya bayyana a jiya Laraba cewa, a daren ranar 10 ga wata, wadannan masu dauke da makamai sun shiga Jamhuriyar Nijar daga kudu maso gabashin kasar Mali, kuma ta hanyoyi guda uku suka kai hari ga wannan sansanin soja, inda suka fafata da dakarun gwamnatin Nijar na tsawon awoyi da dama, al'amarin da ya tilasta sojojin Nijar suka janye daga sansanin. Harin ya kuma haddasa rasuwar masu dauke da makamai 57, amma ya zuwa yanzu, ba wanda ya sanar da daukar alhakin kai wannan hari.

Cikin 'yan shekarun nan, kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi da kungiyoyin 'yan ta'adda wadanda suke da nasaba da kungiyar IS, su kan kai hare-hare a yankunan iyaka dake tsakanin yammacin kasar Nijar, da kasar Mali da kasar Burkina Faso, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane da yawa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China