Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda kasar Sin ta ke saukaka harkokin cinikayya zai taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa
2019-12-11 21:03:08        cri

Yau wata cibiyar nazarin kasar Sin ta fitar da wani rahoto kan yadda kasar Sin take saukaka cinikayya na shekarar 2020, inda aka bayyana cewa, alkaluman saukaka cinikayyar kasar Sin na shekarar 2019 sun kai maki 76.93, adadin da ya kai kaso 5.31 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2017, duk da cewa yanzu haka cinikayyar duniya ta ba gudana yadda ya kamata, amma matsayin saukaka cinikayyar kasar Sin yana daguwa a kai a kai, haka ba ma kawai ya ingiza ci gaban cinikayyar kasar Sin ba, har ma zai taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa.

Da farko, yadda kasar Sin ta ke saukaka harkokin cinikayya ta kara kudin shigar kamfanonin waje, haka kuma za ta kyautata ingancin cinikin wajen kasar Sin, tare kuma da samar da sabbin damammaki ga ci gaban cinikin duniya da karuwar tattalin arzikin duniya, kana za ta taimaka wajen kyautata yanayin kasuwanci a fadin duniya.

Hakazalika, kafin karshen shekarar bana, kasar Sin za ta cimma burin saukaka cinikayya tsakanin kasa da kasa daga duk fannoni, kana za ta kara saukaka ayyukan dake shafar cinikin waje, duk wadannan matakai za su ingiza bunkasuwar cinikin waje mai inganci, haka kuma za ta ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar Sin da ma farfado da tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China