Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na adawa da yadda wasu kasashe ke zargi yanayin hakkin bil Adamarta
2019-12-10 19:24:18        cri

Yau 10 ga watan Disamba, ranar kiyaye hakkin bil Adama ta duniya ce, game da zargin da wasu kasashe ke yi kan yanayin hakkin bil Adama na kasar Sin, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Hua Chunying ta bayyana cewa, wasu kasashe sun kau da kai kan hakikanin abubuwa, inda suke zargi yanayin hakkin bil Adama na kasar Sin kamar yadda suke so, a don haka kasar Sin tana adawa da hakan.

Yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, Hua Chunying ta yi nuni da cewa, al'ummun kasar Sin da kansu sun fi fahimtar yanayin kiyaye hakkin bil Adama da kasarsu ke ciki, bana shekaru 70 ke nan da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, a cikin wadannan shekarun 70, manyan sauye-sauye sun faru a kasar Sin, sha'anin kiyaye hakkin bil Adama shi ma ya samu ci gaba matuka a tarihi, misali al'ummun kasar da yawansu ya kai biliyan daya da miliyan 400 sun cimma burin samun isasshen abinci da sutura, al'ummun kasar da yawansu ya kai miliyan 850 sun kubuta daga kangin talauci, kana gwamnatin kasar Sin ta samar da guraben aikin yi ga al'ummun kasar da yawansu ya kai miliyan 770, ban da haka gwamnatin kasar ita ma ta samar da muhimmin tallafi ga tsofaffin kusan miliyan 250 da nakasassu miliyan 85 da kuma wasu mutanen dake fama da talauci a garuruwa sama da miliyan 60, ana iya cewa, gwamnatin kasar Sin ta cimma burinta na samar da matsakaicin wadata ga al'ummunta, tare kuma da bullo da cikakken tsarin ba da ilmi da tabbacin zaman takewar al'umma da kiwon lafiya da tsarin demokuradiya a fadin kasar baki daya, ba wanda zai musunta wadannan hakikanin abubuwan da suka faru a kasar ta Sin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China