2019-12-10 17:57:01 cri |
Hukumar kula da sararin saman kasar Sin a yau ta fitar da rukunin farko na wasu hotunan da aka dauka ta kusurwa uku ta hanyar bayanan da tauraron dan adam din wanda aka kaddamar kwanan nan samfurin Gaofen-7 ya dauko a binciken da ya gudanar a sararin samaniya.
Tauraron dan adam din, wanda aka harba shi daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar Sin a ranar 3 ga watan Nuwamba, yana da nisan kilomita 506 daga duniyarmu wanda aka tsara zai shafe tsawon shekaru 8. Sama da hotuna 14,000 tauraron dan adam din ya samar.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China