Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin yada labarai na kasashen yamma na nuna halin ko in kula kan wasu ayyukan yaki da ta'addanci a Xinjiang, kuma za su yi girbin abun da suka shuka
2019-12-09 15:56:58        cri
Kwanan baya, kamfanin telibijin na kasa da kasa na kasar Sin CGTN, karkashin jagorancin babban gidan rediyo da telibijin na kasar Sin CMG, ya gabatar da fina-finai biyu na Turanci, karo na farko ne dake bayyana ayyukan ta'addanci na rashin imani da 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi suka aikata a jihar Xinjiang ta kasar Sin, abun da ya tayar da hankalin jama'ar kasar Sin da ta kasashen waje. Amma, wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma dake kokarin danne gaskiyar abun da ke faruwa a Xinjiang, sun yi shiru a wannan karo, kamar ba su jin wani labari dangne da batun. Kafofin na nuna tamkar sun makance kan wannan batu, abin da ya fayyace cewa, kasashen yamma cika hadda Amurka na da fuskoki biyu kan aikin yaki da ta'addanci, wanda hakan wani sako ne mai hadari ga aikin dakile ta'addanci na kasa da kasa. Kana irin wadannan kasashe za su yi girbin abun da suka shuka.

A hakika dai, al'umomin jihar Xinjiang na da hakkin fadin ainihin gaskiyar abun da ke faruwa a jihar, har ila yau, ba a gamu da ayyukan ta'addanci a shekaru 3 a jere a jihar ba, kana yawan masu yawon bude ido da jihar Xinjiang ta karba a watannin 10 da suka gabata ya zarce miliyan 200. Ban da haka yawan kudin shiga da aka samu a jihar Xinjiang a fannin shawon shakatawa ya kai sama da RMB Yuan biliyan 300, wanda ya karu da kashi 40 cikin dari bisa na bara. Ban da wannan kuma, ana samun ci gaba mai yakini ta fuskar kawar da kangin talauci a sassan jihar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China