Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manzon musamman kan batun yankin gabas ta tsakiya na kasar Sin ya yi kira da a ingiza shimfida zaman lafiya a yankin bisa ka'idar kasa da kasa
2019-12-09 14:36:21        cri

Manzon musamman kan batun yankin gabas ta tsakiya na kasar Sin Zhai Jun, ya zanta da manema labarai kwanan baya yayin ziyararsa a Palesdinu, inda ya nanata matsayin da Sin ke dauka kan batun Palesdinu da Isra'ila, kuma ya yi kira ga bangarori daban-daban, da su ingiza aikin shimfida zaman lafiya a yankin bisa ka'idar kasa da kasa.

A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana, Zhai Jun ya yabawa tsarin da Palesdinu ke dauka na warware matsalarta ta hanyar yin shawarwari, da nacewa ga alkiblar "Manufar kasashe biyu", don daidaita bambancin ra'ayi tsakanin Palesdinu da Isra'ila ta hanyar sulhuntawa cikin adalci, bisa kudurorin MDD masu alaka da hakan, da ka'idar samun zaman lafiya ta hanyar ba da filaye, da gudanar da shawarwarin zaman lafiya na kasashen Larabawa, da dai sauran matsaya daya da ka'idojin da aka cimma, da matakin da aka yi kokarin fitar da hanya da bangarorin biyu za su amincewa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China