Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Botswana na shirin amincewa da salon jinya da magungunan gargajiya
2019-12-09 10:07:10        cri
Ministan ma'aikatar lafiya a Botswana Lemogang Kwape, ya ce mahukuntan kasar na duba yiwuwar kafa tsarin doka, wanda zai ba da damar kyautata hanyoyin amfani da magungunan gargajiya, da baiwa masu samar da su damar cin gajiya daga aikin su, tare da sauran magunguna na zamani da ake amfani da su.

Lemogang Kwape, ya ce daukar matakin ya zama wajibi, duba da yadda amfani da magungunan gargajiya, da sauran dabarun warkar da cututtuka ke kara yawaita tsakanin al'umma. Mr. Kwape ya yi wannan tsokaci ne a jiya Lahadi, yayin da yake jawabi a taron masu maganin gargajiya da ya gudana a birnin Francistown, birni na biyu mafi girma a Botswana.

Jami'in ya ce, burin shi ne hade sassan magunguna, da dabarun samar da waraka na gargajiya da na zamani, domin bunkasa kiwon lafiya da rayuwa mai nagarta. Ya ce irin wannan ci gaba zai taimaka wajen kyautata salon samar da jinya ta hanyoyin gargajiya, zai kuma baiwa al'umma damar cin gajiya daga gare su ba tare da fuskantar wani hadari ba.

Mr. Kwape ya kara da cewa, tuni duniya ta ci gaba ta fuskar rungumar dabarun jinya na gargajiya, inda ake kara azama wajen amfani da dabarun zamani da na gargajiya a lokaci guda, kamar yadda hakan ke gudanar a tsarin kiwon lafiya na kasar Sin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China