Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Asusun ECW ya ce ana bukatar dala biliyan 1.8 nan da shekarar 2021 domin tallafawa ilimin yara masu tsananin bukata
2019-12-09 09:23:32        cri

Asusun tallafawa ilimi na ECW, ya ce ana bukatar dala biliyan 1.8 nan da shekarar 2021, domin tallafawa ilimin yara da matasa, su kimanin miliyan 9 dake yankuna masu tsananin bukatar gaggawa, da wadanda ke yankuna masu fuskantar tashe tashen hankula.

Da take karin haske game da hakan, daraktar asusun na ECW Yasmine Sherif ta bayyana cewa, nan da makwanni biyu, wakilan kasashen duniya za su hallara a birnin Geneva, domin gudanar da taron 'yan gudun hijira na kasa da kasa. Yasmine Sherif ta bayyana fatan ganin taron ya zamo wata dama ta sauyawar al'amura baki daya.

ECW, wanda asusun yara na UNICEF ke tallafawa, shi ne asusun kasa da kasa irin sa na farko, da ya mai da hankali ga ayyukan tallafawa ilimi a wurare dake cikin yanayi na bukatar gaggawa.

Wasu masu ruwa da tsaki a fannin ayyukan jin kai da samar da ci gaba, da tallafin sassan gwamnatoci, da masu zaman kan su ne suka kafa asusun, a wani mataki na magance matsalolin da yara da matasa, wadanda yawansu ya kai miliyan 75, ke fuskanta a fannin samun ilimi, a yankunan da ake fama da rikice rikice. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China