Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu kafofin watsa labarun kasashe yammacin duniya sun kyale bidiyo game da yaki da ta'addanci a yankin Xinjiang
2019-12-08 19:50:16        cri
A kwanakin baya, kafar watsa labaru ta CGTN ta kasar Sin ta gabatar da bidiyo guda biyu game da yaki da ta'addanci a yankin Xinjiang ta harshen Turanci. Bidiyon farko ya bayyana hakikanin batun harin ta'addanci da aka kai ga birnin Urumqi a ranar 5 ga watan Yuli na shekarar 2009, da harin ta'addanci da aka kai ga birnin Beijing a ranar 28 ga watan Oktoba na shekarar 2013 da kuma harin ta'addancin da aka kai birnin Kunming a ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2014. Bidiyon daban ya shaida ayyukan kungiyar ta'addanci ta gabashin Turkiyya wato East Turkistan Islamic Movement ETIM da aka yi a yankin Xinjiang. Amma ban da gidan rediyon kasar Faransa, manyan kafofin watsa labaru na kasashe yammacin duniya ba su gabatar da bidiyon biyu ko bayar da labarai game da su ba.

An jaddada cewa, batun yankin Xinjiang ba batun kabila, ko addini, ko hakkin bil Adama ba ne, shi batu ne na yaki da ta'addanci da 'yan aware. Wasu kafofin watsa labaru da 'yan siyasa na kasashe yammacin duniya ba su maida hankali ga barazanar da ake fuskanta a yankin Xinjiang ba, sun zargi kasar Sin ta hanyar fakewa da batun hakkin bil Adama, da demokuradiyya, da samun 'yanci, suna yunkurin kawo baraka ga kasar Sin. Wannan aiki bai dace da aikin yaki da ta'addanci ba, a karshe dai za su samun mugun tasiri a sakamakon hakan. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China