Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasuwar fasahar AI ta Sin za ta kai dala biliyan 11.9 nan da 2023
2019-12-08 16:31:40        cri

Wata sabuwar takardar bayani da aka fitar ta nuna cewa, ana hasashen kasuwar kasar Sin a fannin fasahar kwaikwayon tunanin dan adam wato AI, za ta kai matsayin dala biliyan 11.9 nan da shekarar 2023.

Alkaluman dake kunshe cikin takardar bayanin da kamfanin fasaha na kasa da kasa wato IDC da wani kamfanin fasaha na kasar Sin QbitAI suka fitar sun nuna cewa, sakamakon nagartattun manufofi, ana sa ran kasuwar fasahar AI ta kasar Sin za ta kai kashi 12 bisa 100 a duniya a shekarar nan ta 2019, inda ta karu da kashi 64 bisa 100 a shekara guda, hakan ya sa ta kasance kasuwar fasahar ta biyu mafi girma a duniya.

Takardar ta ce, kamfanonin kasar Sin sun kara zuba jarinsu a fannin fasahar AI cikin wannan shekarar, kuma manhajojin fasahar AI suna karuwa cikin sauri. Bangarorin da ake sa ran kasuwar fasahar AI ta kasar Sin za ta mayar da hankali sun hada da bangarorin ba da hidima, da kiwon lafiya da kuma harkokin sadarwa.

Bugu da kari takardar bayanin ta yi hasashen cewa, kasuwar fasahar za ta iya kaiwa dala biliyan 4.25 nan da shekarar 2020, tare da tsammanin samun karuwar kashi 51.5 a duk shekara.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China