Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masar da Sin za su zurfafa hadin gwiwa wajen yaki da rashawa
2019-12-08 16:09:48        cri

Kasashen Masar da Sin sun himmatu wajen yaki da ayyukan rashawa, kana za su kara karfafa hadin gwiwa wajen yaki da rashawa ta hanyar yin cudanya tsakanin kwararrun sassan biyu, wata kwararriyar kasar Masar ta bayyana hakan a zantawarta da kamfanin dillancin labaru na Xinhua.

Nadia Helmy, farfesa a fannin kimiyyar siyasa ta jami'ar Beni-Suef ta kasar Masar, ta yabawa kyakkyawan sakamakon da hukumar yaki da rashawa ta kasar Sin ta samu wanda jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta CPC ta kaddamar a wasu 'yan shekaru da suka gabata.

Kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba a bangaren yaki da ayyukan rashawa tun bayan da CPC ta kaddamar da gagarumin shirinta na yaki da ayyukan rashawa na ba sani ba sabo, wanda ya shafi tuhumar manya da kananan jami'an gwamnatin kasar, wanda kasar Masar za ta koyi darasi daga shirin, in ji kwararriyar.

Helmy ta ce, hukumar yaki da rashawa ta kasar Sin ta samu nasarar kwato makudan kudaden da aka sace daga baitil malin kasar, kana ta sha alwashin yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya domin kamo wasu jami'an gwamnatin kasar da suka tsere zuwa ketare wadanda ake tuhumarsu da laifuffukan cin hanci da rashawa.

Ta ba da shawarar zurfafa hadin gwiwa tsakanin Masar da Sin don yaki da ayyukan rashawa ta hanyar musayar kwararrun masana na hukumar yaki da rashawa na kasar Sin CCDI, da takwarorinsu na kasar Masar na hukumar ACA, wacce ta samu nasarar bankado wasu manyan jami'an kasar da ake zargi da aikata laifukan rashawa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China