Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mene ne matsala ga aikin daidaita tunani?
2019-12-07 17:26:41        cri

Me kuke gani game da aikin daidaita tunani ga masu aikata kananan laifuka?

Shin akwai wata hanyar da ta fi dacewa wajen shawo kan laifuka, idan akwai hanya mafi inganci ta samar da darussan kawar da tsattsauran ra'ayi idan sun nuna nadama ta gaskiya ga abin da suka aikata? Idan sun yarda su koyi sabbin dabaru don haka zasu iya komawa rayuwar fararen hula?

Wannan shi ne wani aikin da kasar Sin ke yi a jiharta ta Xinjiang cikin shekaru ukun da suka gabata. Sai dai majalisar wakilai ta Amurka ta zartar da wani shirin doka wanda ya soki manufofin Sin game da jama'arta 'yan kabilar Uyghur, wai kasar na aikata laifin take hakkin bil adama da na addini.

Dokar da ake kira "Uyghur Act of 2019" ta yi watsi da kokarin da gwamnatin Sin take yi a fannin dakile ta'addanci, sannan ta bukaci daukar matakan magance abin da ta kira "tsare 'yan Uyghur sama da miliyan daya ba gaira ba dalili."

Wannan ikirarin daidai yake da cewa manufar da kasar Amurka ke dauka, ta nemi wani da ya yi aikin tilas na samar da hidimomi ga al'umma, saboda wasu kananan laifuffukan da ya aikata, kuskure ne. Ko da yake manufar da aka dauka a jihar Xinjiang ta kasar Sin, inda ba kawai mutane suna koyan darasi ba ne har ma da wasu fasahohin sana'a masu amfani, ya fi kama da shirin "dakatar da tunani maras kyau da daina aikata laifi" na kasar Birtaniya. Ta hanyar matakan daidaita tunani, jihar Xinjiang tana kokarin taimakawa wadanda suka aikata kananan laifuka, don neman kawar da tsattsauran ra'ayi, da rigakafin abkuwar ayyukan ta'addanci.

Me zai faru idan kasar Sin ta zartar da wani kudurin doka na suka kan manufofin kasar Amurka game da masu aikata kananan laifuka? Ina tambaya kawai, me ke damun aikin daidaita tunani? Kawai saboda kasar Sin tana yin haka ne ya sa wasu kasashen yamma ke daukar ra'ayi na kin amincewa? Wannan shine abin da ake kira nuna bambanci, gami da rashin sanin ya-kamata. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China