Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a kawar da ta'addanci a jihar Xinjiang sakamakon wadata da zaman karko
2019-12-07 16:33:13        cri

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a a yau Asabar ya gabatar da wani sharhi mai taken "Za a kawar da ta'addanci a jihar Xinjiang sakamakon wadata da zaman karko".

Sharhin ya ce, a 'yan kwanakin da suka wuce, majalisar wakilan kasar Amurka ta shafa kashi kan ayyukan kasar Sin na yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi, amma zaman karko da wadata da aka samu a jihar Xinjiang ta kasar Sin sun kasance abubuwan shaida ne masu karfi wajen fallasa karyar Amurka, ko shakka babu wasu 'yan siyasar Amurka ba zasu yi nasara ba a yunkurinsu na hana ci gaban kasar Sin ta hanyar amfani da batun Xinjiang.

Sharhin ya nuna cewa, bisa tushen koyon fasahohin da kasa da kasa suka samu wajen yaki da ta'addanci, kasar Sin ta dauki jerin matakan yaki da ta'addanci na yin rigakafi a Xinjiang. Gwamnatin jihar Xinjiang ta kafa cibiyoyin bada ilmi da horo kan sana'o'i, da nufin ceto mutanen da aka yiwa tasiri sakamakon ta'addanci da nuna tsattsaraun ra'ayi, kana da samun kwarewar fasahohi, hakan zai basu damar shiga zaman al'umma yadda ya kamata. Bisa matakai masu amfani da aka dauka, ba a samu hare haren ta'addanci ba a cikin shekaru 3 da suka gabata a jere, a cikin watanni 10 na farkon shekarar bana, adadin mutanen kasar Sin da na kasashen ketare da suka je yawon shakatawa a Xinjiang ya wuce miliyan 200, wato ya karu da kusan kashi 43 cikin 100 bisa na makamancin lokacin bara, wannan ne kuma ya shaida cewa, ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a wurin.

Baya ga haka, sharhin ya jaddada cewa, a cikin shekaru 30 da suka wuce, matsakaicin yawan kudin shiga da mazauna jihar Xinjiang suka samu ya ninka sama da sau 100. Wata jihar Xinjiang mai wadata da zaman karko zai kara samar da alheri ga jama'ar wurin daga kabilu daban daban da yawansu ya wuce miliyan 25, tabbas ne kuma zai kawar da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi da kuma haskaka hanyar bunkasuwar jihar a nan gaba. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China