Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
ISO ya gamsu da yadda birnin Beijing ke shirya karbar gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi
2019-12-06 10:57:41        cri

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta duniya Thomas Bach, ya bayyana cewa, takardar shaida da kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi da za a yi a Beijing a shekarar 2022 ya samu, alama ce da ke nuna kudirin Beijing na ganin an shirya wannan gasa cikin nasara.

Bach ya ce, kwamitin na Beijing, shi ne kwamitin shirya gasa na farko da ya samu irin wannan takardar shaida.

Ita dai takardar shaidar ta ISO 20121, an bullo da ita ne yayin gasar Olympics da aka shirya a birnin London a shekarar 2012, da nufin tabbatar da cewa, gasannin sun mayar da hankali kan muhimman fannonin zamantakewa, tattalin arziki da tasirin yanayi, sannan za ta bar tasiri mai kyau da za a iya yin koyi da shi.

A matsayinta na daya daga cikin biranen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi a harkokin wasanni na MDD, gasar ta Beijing ta shekarar 2022, ta hade sassa masu muhimmanci yayin gudanar da ayyukanta, kamar alkinta ruwa da isashen makamashi da kula da hayakin carbon.

A cewar, Juan Antonio, shugaban hukumar tsare-tsare ta IOC na gasar Beijing ta shekarar 2022, takardar shaidar, ba kawai ta aike da sako mai karfi game da kudirin birnin Beijing na samar da ci gaba mai dorewa ba, har ma ta nuna kudirin kasar Sin". Domin ta bude hanya ta shirya wasanni daban-daban a kasar Sin. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China