Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tabbas ne Amurka za ta ci tura a yunkurinta na amfani da batun Xinjiang don hana ci gaban Sin
2019-12-05 19:48:17        cri
A yau Alhamis babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ya gabatar da sharhi mai taken "Tabbas ne Amurka za ta ci tura a yunkurinta na amfani da batun Xinjiang don hana ci gaban Sin".

Sharhin ya ce, majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas da dokar hakkin bil Adama kan yankin Xinjiang na Uygur ta shekarar 2019, matakin da ya kasance tsoma baki ne cikin harkokin gida na kasar Sin kiri da muzu, yana kuma shafa wa kasar Sin kashin kaji kan manufofinta na gudanar da harkokin yankin Xinjiang, da matakan da ta dauka na yaki da ta'addanci, da kuma yadda halin hakkin bil Adama yake a yankin. Hakan na isar da sako na kuskure ga masu ta'addanci.

Shirhin ya ce babban burin Amurka shi ne lalata ci gaba da zaman karko na yankin Xinjiang, da kawo cikas ga kokarin al'ummar kasar Sin na neman farfadowa. Kasar Amurka ta kara bayyana nufinta na hana ci gaban kasar Sin, ta hanyar amfani da batun Xinjiang, amma ko shakka babu za ta ci tura.

Baya ga haka, sharhin ya nuna cewa, batun Xinjiang, ba batun ne da ya shafi kabilu, addinai da kuma hakkin bil Adama ba, a maimakon haka yana da alaka ne da aikin yaki da ta'addanci da ra'ayin 'yan aware.

Matakin majalisar wakilan Amurka na zartas da wannan doka ba kawai ya musunta nasarorin da aka cimma wajen yaki da ta'addanci a yankin Xinjiang ba, har ma ya lalata hadin kai a tsakanin kasa da kasa wajen yaki da ta'addanci. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China