Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Sin ya taimakawa Nijeriya gina jami'ar koyon ilmin sufuri ta farko a Afrika
2019-12-05 14:09:34        cri


Kwanan baya a garin Daura na jihar Katsina dake tarayyar Najeriya, kamfanin CCECC na kasar Sin, ya aza tubalin aikin gina jami'ar koyon ilmin sufuri a Nijeriya, wadda ta kasance irinta na farko a nahiyar Afrika, matakin da ya tabbatar da tsarin hadin kai a fannin gudanar da manyan ayyuka 8 da aka gabatar a taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika. Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya halarci bikin, inda ya nuna godiya da taimakon da Sin take baiwa kasarsa.

Jami'ar koyon ilmin sufuri ta Nijeriya tana daya daga cikin ayyukan da za su taimaka wajen zamanantar da layin dogo na Nijeriya da kamfanin CCECC ya ba da taimako wajen gina su. Yayin bikin aza tubali, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya nuna cewa, jami'ar ta kasance irinta na farko a nahiyar Afrika, wadda ake sa ran za ta samar da kwararru a fannin zirga-zirga da sufuri, don rage gibin da kasar ke fuskanta na karancin ilmomin kimiya da fasaha a wannnan fanni. Ya ce: "Wannan aiki ya tabbatar da alkawarin da kamfanin CCECC ke yi na daukar nauyin taimakawa al'ummar Nijeriya, da kuma hakikanin matakin da ya dauka na ingiza hadin kan kasashen biyu. Ina godiya sosai da taimakon da gwamnatin kasar Sin take ba mu, musamman ma kokarin da kamfanin CCECC ya yi, kuma na jinjinawa ayyuka masu inganci cikin lokaci da ya dade yana gudanarwa, matakin da ya sheda hadin kan kasashen biyu a dogon lokaci."

A jawabinsa yayin bikin, jakadan Sin dake Nijeriya Zhou Pingjian ya nuna cewa, Sin tana tsayawa tsayin daka kan hadin kan Sin da Afrika bisa daidaito da adalci da zumunci da kuma sahihanci, Kasar Sin ta dukufa kan tabbatar da sakamakon ci gaban da aka samu a gun taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika, da kuma hadin gwiwar kasashen biyu bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kuma goyon bayan Nijeriya wajen tabbatar da samun bunkasuwa ta hanyar dogaro da kai. Ya ce:

"Gina wannan jami'a yana daya daga cikin matakan da gwamnatin tarrayar Nijeriya ke dauka wajen shigo da kimiya da fasahar sufurin jirgin kasa da sa kaimi ga kara karfinta, matakin da aka yi maraba da shi. Kamfanin CCECC ya sheda karfinsa na zama wata gada wajen ingiza zumuncin Sin da Nijeriya."

Kamfanin na kasar Sin ya dauki nauyin gina wannan jami'a ce bisa bukatar ma'aikatar sufuri ta kasar Nijeriya, da zummar taimakawa Nijeriya wajen kyautata tsarin samar da kwarewa a fannin zirga-zirgar jirgin kasa, ana kuma sa ran hada kai da sauran jami'o'i kan darussa da zai gabatar nan gaba, don inganta harkokin koyarwa da baiwa dalibai dama mai kyau kan aikin gwaje-gwaje, ta yadda za a samar da kwararru a fannin ayyukan layin dogo na zamani a kasar. Babban direktan reshen Najeriya na CCECC Jiang Yigao ya nuna cewa:

"Gina wannan jami'a na daya daga cikin alkawuran da kamfaninmu ya yi ga sauke nauyin dake wuyanmu na taimakawa bunkasuwar al'ummar Nijeriya, CCECC zai ci gaba da hada kai da gwamantocin sassan kasar don dukufa kan bunkasuwar kasar. Muna farin ciki da alfahari sosai na gudanar da wannan babban aiki."

A nasa jawabin, ministan sufuri na Najeriya Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ta fahimci muhimmacin ilmi ga ayyukan manyan ababen more rayuwa da yadda za a yi amfani da su a nan gaba. Ana sa ran kasar za ta iya kula da manyan na'urorin sufurin kasar nan gaba, ciki hadda jirgin kasa da sauransu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China