2019-12-04 20:01:17 cri |
Sharhin ya ce, majalissar wakilan Amurka ta zartas da shirin doka kan manufofin hakkin dan Adam na Uygur na shekara ta 2019, inda ta jirkita gaskiya game da hakkin dan Adam a jihar Xinjiang ta kasar Sin, da shafa kashin kaji ga kokarin da gwamnatin kasar ta yi na kawar da masu tsattsauran ra'ayi da yaki da ayyukan ta'addanci, a wani yunkuri na kalubalantar manufofin gwamnatin kasar Sin kan Xinjiang. Sin na nuna matukar takaici gami da adawa da hakan.
Sharhin ya jaddada cewa, gwamnati gami da al'ummar Sin, suna tsayawa tsayin daka wajen kare ikon kasa, da yanayin tsaro, gami da moriyar ci gabanta. Harkokin Xinjiang, harkokin cikin gida ne na kasar Sin zalla, kana kuma nasarori da ci gaban da Xinjiang ta samu a bayyane suke, wadanda Amurka ba za ta iya kawar da su ba. A sabili da haka, ya kamata Amurka ta gyara kuskuren da ta aikata ba tare da bata lokaci ba, da dakatar da "shirin doka" zama ainihin doka, tare kuma da dakatar da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar amfani da batun Xinjiang, don kaucewa ta'azzarar dangantakar Sin da Amurka.(Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China