Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron sauyin yanayi: Akwai kalubaloli da dama a gabanmu wajen magance sauyin yanayi
2019-12-04 14:28:00        cri

A halin yanzu, ana gudanar da taron kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi na MDD karo na 25 a birnin Madrid, fadar mulkin kasar Sifaniya. A jiya Talata, shugaban tawagar wakilan kasar Sin ya gabatar da bayani game da taron na wannan karo.

Ko da an bude taron kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi na MDD karo na 25 a ranar 2 ga wata, amma tun a makon da ya gabata an riga an fara yin shawarwari tsakanin bangarori daban daban, kuma rahotanni na cewa, ban da taron kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar karo na 25, za a kuma yi taruka guda hudu game da abin ya shafa, inda mahalarta za su tattauna kan batutuwa kimanin guda 80, da suka shafi kudade, fasahohi, matakan warware matsaloli da ayyukan gona da dai sauransu. Kana, alkaluman kididdigar da ofishin sakatariyar taron ya fidda, sun nuna cewa, a halin yanzu, akwai mutane sama da dubu 26 da suka yi rajistar halartar taron, ciki har da wakilan bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi, da mambobin kasashe masu sa ido da sauransu, lamarin da ya nuna cewa, gamayyar kasa da kasa suna mai da hankali kware da gaske kan babban taro na wannan karo.

A lokacin taro na 24 da aka yi a bara, bangarori daban daban sun zartas da galibin yarjeniyoyin da aka cimma a cikin "Yarjejeniyar Paris", amma akwai wasu batutuwan da za a ci gaba da tattaunawa a taro na bana. Kuma taro na bana, shi ne na karshe da za a yi kafin a fara aiwatar da "Yarjejeniyar Paris" a hukumance, shi ya sa, batun yadda za a aiwatar da yarjejeniyar ba kawai ya kasance batu mafi muhimmanci da za a tattauna ba, har ma ya kasance batu mai wahalar gaske. Mataimakin babban sakataren tawagar wakilan kasar Sin, kana mataimakin shugaban ofishin kula da yanayi na ma'aikatar harkokin yanayi da halittu ta kasar Sin, Lu Xinming ya bayyana cewa, "Wasu kasashe suna ganin cewa, kammala tattaunawa kan sharadi na shida na "Yarjejeniyar Paris", watau yadda za a aiwatar da tsarin kasuwanni, shi ne babban aikin dake gabanmu. Amma a halin yanzu, bangarori daban daban da abin ya shafa, ba su iya cimma matsayi daya kan wannan batu ba. Kana, a halin da muke ciki yanzu, mai iyuwa ne, ba za mu iya kammala shawarwari kan wannan batu bisa lokacin da aka tsara ba."

Haka kuma, ya ce, a halin yanzu, sabanin dake tsakanin kasashe masu ci gaba da kasashe masu tasowa yana cikin sharadi na shida, kuma zai yi wuya matuka a cimma daidaito a tsakaninsu.

Ban da sabanin da aka samu kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar, har ma, a kwanan baya an gabatar da wata sabuwar shawara game da sabon buri da ake fatan cimmawa dangane da sauyin yanayi. Inda aka ce, ya kamata mu kayyade karuwar zafin duniya zuwa kasa da digiri 1.5 na ma'aunin Celsius zuwa karshen wannan karni, a maimakon digiri 2℃ da aka tsara cikin "Yarjejeniyar Paris".

Dangane da wannan batu, mataimakin shugaban tawagar wakilan kasar Sin, kana manzon musamman na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin kan shawarwarin sauyin yanayi, Sun Jin, ya bayyana cewa, "A halin yanzu, babban aikin dake gabanmu shi ne aiwatar da wannan yarjejeniya, idan muka fara bijiro da wani sabon buri, wanda ya keta burin da bangarori daban daban suka tsara bisa shawarwarin da suka dade suna yi, zai sa aikin aiwatar da yarjejeniyar zama aikin banza. A hakika, cikin aya ta biyu na "Yarjejeniyar Paris", an bayyana cewa, ya kamata mu rage karuwar zafin duniya zuwa kasa da digiri 2℃, kuma ya dace mu dukufa wajen rage karuwar zafin duniya zuwa kasa da digiri 1.5℃. Haka zalika, cikin yarjejeniyar, mun jaddada cewa, ba kawai mu mai da hankali kan rage adadin iska mai gurbata muhalli da za a fitar ba, har ma, mu mai da hankali kan neman dauwamammen ci gaba, lura da kasashen dake kokari wajen kawar da talauci, da kuma kudaden da kasa da kasa suke bukata, dukkansu bukatu ne dake cikin "Yarjejeniyar Paris". Kawai mai da hankali kan burin rage iska mai gurbata muhalli bayan shekarar 2020, bai dace da babban buri na "Yarjejeniyar Paris ba". "

Ban da haka kuma, wakilan kasar Sin suna ganin cewa, babban aikin dake gabanmu ba fito da wani sabon buri ba ne, amma aiwatar da burin da muka riga muka tsara, musammam na yin nazari kan matakan da kasashe masu ci gaba suka dauka kafin shekarar 2020.

Kasar Sin ba kawai kasa ce mai tasowa mafi girma ba, jagora ce a yunkurin da ake na magance matsalar sauyin yanayi. Sun Jin ya kara da cewa, a ko da yaushe, kasar Sin tana jaddada cewa, ya kamata mu yi bayani da aiwatar da Yarjejeniyar Paris yadda ya kamata, kuma tana fatan ba da gudummawa a wannan aiki.

Bugu da kari, wakilan kasar Sin sun ce, ya kamata bangarori daban daban su cika alkawuran da suka dauka a Yarjejeniyar Paris bisa ka'idar adalci, da nuna fahimta ga halayen musammam da sauran kasashe suke ciki. Domin haka ne kawai za a yi nasarar aiwatar da "Yarjejeniyar Paris" kamar yadda ake fata, da kuma daukar matakai cikin himma da kwazo, don karfafa hadin gwiwar kasa da kasa. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China