Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta ci gaba da mara baya ga ayyukan hukumar IAEA
2019-12-03 10:36:31        cri
Zaunannen wakilin Sin a hukumomin MDD da na sauran kungiyoyin kasa da kasa da ke Vienna, Wang Qun, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da mara baya ga ayyukan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, tare da sa ran aiki kafada da kafada da sabon Darakta Janar na hukumar, Rafeal Mariano Grossi.

Zauren musamman na hukumar IAEA ne ya nada Rafeal Mariano Grossi, jami'in diflomasiyya na kasar Argentina, a matsayin sabon Darakta Janar na hukumar.

Wang Qun ya taya Rafeal Mariano Grossi murnar samun mukamin, tare da godewa mukaddashin daraktan Janar na hukumar, bisa gudunmmawar da ya bayar.

Wang Qun ya ce duniya na cikin wani yanayi na gagarumin sauye-sauye, kuma IAEA na da muhimman nauyi a wuyanta, na tabbatar da amfani da makamashin nukiliyar ta hanyar da ta dace da kare yaduwar makaman nukiliya da kuma taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya.

Ya kara da cewa, suna fatan sabon Darakta Janar din, zai kiyaye ka'idojin aiki da tabbatar da adalci ba tare da bangaranci ba da nuna kwarewa da kuma hada kan dukkan mambobin hukumar. Haka zalika, suna sa ran zai jagoranci hukumar wajen magance kalubale daban-daban da inganta ayyukanta bisa daidaito da sauke dukkan nauyin dake bias wuyanta da kuma bada gagarumar gudunmmawa wajen inganta amfani da makamashin nukiliya ta hanyar wanzar da zaman lafiya da samar da ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China