Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi alkawarin tara sama da dala miliyan 55 a taron AU don yakar Ebola
2019-12-03 09:45:48        cri
A jiya Litinin an gudanar da taron dandalin kungiyar tarayyar Afrika AU a helkwatar kungiyar dake Addis Ababa, inda aka yi alkawarin samar da kudi sama da dala miliyan 55 domin shirin yaki da cutar Ebola a Afrika.

Taken taron shi ne, "Dandalin yaki da Ebola a Afrika na bangarori masu zaman kansu da masu bada taimako" shugaban gudanarwar kungiyar ta AU, Moussa Faki Mahamat, shi ne ya kira taron, da nufin neman taimakon kudade daga kasashe mambobin kungiyar ta AU da sauran bangarori masu bada taimako domin taimakawa shirin yaki da annobar kwayar cutar Ebola (EVD) a jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC), da kuma hana cutar bazuwa zuwa sauran sassa na duniya.

Da take jawabi a taron manema labarai bayan kammala dandalin, kwamishiniyar AU ta sashen jin dadin al'umma, Amira Elfadil, ta ce, taron ya samu gagarumar nasara kuma mahalarta taron sun yi alkawurran bayar da taimakon kudade da sauran nau'in taimako iri daban daban.

Kwamishiniyar ta ce, babu wani goyon baya da ya wuce irin wanda mahalarta taron suka nuna na bayar da taimakon kudi da sauran nau'ikan taimako, kuma hakan zai taimakawa gwamnatin Kongo DRC a shirinta na yaki da cutar Ebola, har ma da sauran cutuka. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China