Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An dawo da gawarwakin mutanen da suka yi gudun hijira daga Vietnam zuwa Birtaniya
2019-12-01 16:12:57        cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Vietnam ta ce, an dawo da dukkan gawarwaki ko tokar gawar mutanen da suka mutu sakamakon gudun hijirar da suka yi daga Vietnam zuwa Birtaniya gida wato Vietnam, wadanda aka riga aka mika su zuwa ga 'yan uwansu.

Rahotanni sun ce, an kai kashin farko na gawarwaki 16 zuwa fadar mulkin kasar Vietnam wato Ha Noi a ranar 27 ga watan Nuwamba, yayin da aka kai sauran wasu gawarwarki ko tokar gawarwakin mamata 23 gida a ranar 30 ga watan Nuwamba. 'Yan uwan mamatan za su binne gawarwakin a jihohinsu na asali a Vietnam.

Tun a ranar 23 ga watan Oktobar bana, 'yan sandan kasar Birtaniya suka gano wasu gawarwaki 39 a wata babbar motar dakon kaya a gundumar Essex dake kudu maso gabashin kasar. Daga baya a ranar 7 ga watan Nuwamba, ma'aikatar tsaron jama'a ta kasar Vietnam ta sanar da cewa, kasashen biyu sun tabbatar da cewa dukkan mamatan 'yan asaslin Vietnam ne.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China