2019-11-30 16:10:21 cri |
Rahotannin sun ce 'yan sandan Birtaniya sun san mutumin da ake zargi kuma an yi ammana yana sanye da alamar gidan yari.
Bayan aukuwar harin, 'yan sandan birnin London sun ayyana shi a matsayin harin ta'addanci.
'Yan sandan sun kuma harbe mutumin da ake zargi da dabawa mutane wuka a kan gadar birnin London dake cibiyar birnin a jiya Juma'a.
'Yan sandan sun yi ammana cewa mutumin da ake zargin na dauke da ababen fashewa a jikinsa.
Maharin ya kashe fararen hula 2 yayin da wasu 3 ke asibiti, sanadiyyar daba musu wuka da ya yi.
Biyo bayan harin, Firaministan Birtaniya Boris Johnson, ya ce za a kara girke 'yan sanda a tituna. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China