Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala taron kawar da talauci karkashin FOCAC
2019-11-30 15:51:19        cri
Daga ranar 28 zuwa ta 29 ga watan Nuwamban da muke ciki, aka yi taro kan kawar da talauci da neman ci gaba karkashin tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka FOCAC na shekarar 2019, a birnin Kampala na kasar Uganda, inda wakilai fiye da 150 da suka fito daga kasashen Afirka, da kasar Sin, da wasu kungiyoyin kasa da kasa, suka halarci taron, tare da musayar fasahohi a fannonin rage talauci da neman ci gaban al'umma.

A wajen taron, shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni ya yi jawabi, inda ya ce don neman fitar da miliyoyin mutane daga kangin talauci a nahiyar Afirka, ana bukatar raya wasu manyan fannoni 4, wato raya aikin gona don biyan bukatar kasuwanci, da raya masana'antu, da bangaren samar da hidimomi, da kuma sadarwa. A cewar sa, ya kamata a daidaita harkokin wadannan fannoni 4 da ayyukan hukumomin gwamnatoci, ta yadda za su hada kai a kokarin kawar da talauci.

A nasa bangare, Bience Gawanas, mataimakin babban magatakardan MDD kuma mashawarcinsa a fannin harkokin nahiyar Afirka, ya ce karkashin tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka FOCAC, gami da shawarar da kasar Sin ta gabatar ta "Ziri Daya da Hanya Daya", kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a kokarin taimakawa kungiyar kasashen Afirka AU wajen tsara ayyukan more rayuwar al'umma, da dunkulewar nahiyar Afirka waje guda, da samar da karin damammakin ciniki da guraben ayyukan yi, da raya tattalin arziki gami da rage talauci a nahiyar ta Afirka.

A nasa bangaren, Chen Zhigang, mataimakin darektan ofishin dake jagorantar aikin rage talauci karkashin majalisar gudanarwar kasar Sin, cewa ya yi, a cikin shekaru 10 da suka wuce, taron rage talauci da neman ci gaba na Sin da Afirka, ya riga ya zama wani muhimmanin dandali na musayar ra'ayi ta fuskar kau da talauci, tsakanin Sin da Afirka. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China