Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gabatar da sakon taya murnar tunawa da ranar goyon bayan al'ummar Palesdinu
2019-11-28 11:25:33        cri

MDD ta gudanar da taron tunawa da ranar goyon bayan al'ummar Palesdinu ta kasa da kasa a jiya Laraba, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya buga waya domin taya murnar gudanar da wannan taro.

Cikin tsokacin da ya gudanar, Xi Jinping ya nuna cewa, batun Palesdinu muhimmin mataki ne a batun yankin gabas ta tsakiya. Yadda za a daidaita wannan batu na Palesdinu cikin adalci a dukkanin fannoni, a kokarin tabbatar da yin zama tare cikin lumana, da samun bunkasuwa tare tsakanin Palesdinu da Isra'ila ya dace da muradun al'ummar duniya.

Xi ya jaddada cewa, Sin sahihiyar abokiyar Palesdinu ce, wadda ke tsayawa tsayin daka kan manufar wanzar da zaman lafiya tsakanin Palesdinu da Isra'ila. Har ila yau, Sin na goyon bayan kokarin da Palasdinawa suke yi na farfado da hakkin al'umma da ayyukansu yadda ya kamata, da kuma amincewa da kafa kasar Palesdinu mai 'yancin kai mai hadkwatar birnin Kudus na gabas, bisa iyakar kasa da aka kai ga matsaya daya a kan ta a shekarar 1967.

Ban da wanann kuma, Sin na son hadin kai tare da kasa da kasa don taka rawa wajen ingiza shawarwarin bangarorin biyu, bisa aniyar tabbatar da zaman lafiya mai dorewa daga duk fannoni cikin adalci a yankin gabas ta tsakiya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China