Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'ai: Ya kamata Afrika su koyi darasi daga shirin kawar da talauci na kasar Sin
2019-11-28 10:22:29        cri
Wakilan gwamnatocin kasashen Afrika da Sin da kwararrun masana da shugabannin bangarori masu zaman kansu za su gudanar da taron musayar kwarewa da nufin duba hanyoyin tsame miliyoyin al'ummar Afrika daga talauci.

Taron karawa juna sanin game da kawar da talauci da bunkasa cigaba na kasashen Afrika da Sin na shekarar 2019 za'a gudanar tsakanin 28-29 ga watan Nuwamba. Za'a shirya taron ne karkashin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika wato (FOCAC), wanda ya kunshi hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika daga dukkan fannoni.

Mashirya shirin sun gabatar da kwarya-kwaryar taron manema labarai a jiya Laraba, inda suka bayyana cewa ya dace Afrika ta koyi wasu muhimman darrusa daga kasar Sin, wacce take da matsayin cigaba iri daya da na Afrika a shekarun 1970, amma a halin yanzu ita ce kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Li Xin, daraktar sashen hulda da kasashen waje ta hukumar yaki da fatara ta kasa da kasa dake kasar Sin tace, kasar Sin ta aiwatar da dabarun kawar da talauci ta hanyar tuntubar dukkan iyalai dake fama da yanayin talauci domin sanin hakikanin kalubalolin dake damunsu kuma ta yaya suke tunanin za su iya fita daga kangin talaucin.

A cewar Li, kasar Sin ta aiwatar da shirinta na yaki da talauci a matsayin daya daga cikin dukkan manufofinta na raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'ummarta.

Ta ce shugabannin kasar Sin sun mayar da shirin yaki da talauci a matsayin babbar ajandar raya cigaban kasar, sun bada fifiko matuka ga shirin yaki da talauci.

Christopher Kibanzanga, ministan aikin gona na kasar Uganda ya fadawa manema labarai cewa tuni kasashen Afrika sun fara koyon darasi daga kasar Sin game da batun shirin kawar da talauci.

Sama da wakilai 150 da suka hada da wakilai 50 daga kasar Sin da wakilai 70 daga Afrika sai wakilai 30 daga kungiyoyin kasa da kasa ne ake sa ran zasu halarci taron wanda shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni zai gabatar da jawabin bude taron. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China