Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan mutunta da kare ikon mallakar ilmi ga juna tsakanin ta da kasashen ketare
2019-11-26 14:35:40        cri

Kwanan baya, babban ofishin kwamitin tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, da babban ofishin majalissar gudanarwar Jamhuriyyar Jama'ar kasar Sin, sun gabatar da "Shawarwari kan inganta ayyukan kare ikon mallakar ilmi", inda suka tsara shirin yadda za a aiwatar da wannan aiki. Wani jami'i mai kula da wannan aiki a hukumar ikon mallakar ilmi ta kasar Sin ya bayyana a jiya Litinin a birnin Beijing cewa, duk da cewar kasar Sin tana mutunta da kuma kare ikon mallakar ilmi na kasashen ketare, a hannu guda kasar tana fatan gwamnatocin kasashen waje za su iya kiyaye ikon mallakar ilmi na kasar Sin.

A halin yanzu, kasar Sin ta riga ta shiga cikin manyan yarjejeniyoyin ikon mallakar ilmi na kasa da kasa, ta kuma kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da takardun fahimtar juna da kasashe, yankuna da kungiyoyin kasa da kasa sama da 60, haka kuma, ta kafa dangantakar hadin gwiwa da mambobin kungiyoyin ikon mallakar ilmi na kasa da kasa guda 50 a hukumance.

Shawarwarin kan inganta ayyukan kare ikon mallakar ilmi da aka fidda, za su karfafa hadin gwiwar Sin da kasa da kasa, da kyautata hanyoyin yin mu'amala da masu kula da aikin na kasar Sin da na kasashen waje, da karfafa aikin ba da taimako ga wadanda suke neman kare ikon mallakar ilmi a kasashen waje, da kuma inganta aikin yin mu'amala kan harkar ikon mallakar ilmi. Dangane da wannan harka, mataimakin shugaban hukumar ikon mallakar ilmi ta kasar Sin, Gan Shaoning ya bayyana cewa, "Baya ga cewa kasar Sin tana mutunta da kiyaye ikon mallakar ilmi na kasashen waje, haka kuma, tana fatan gwamnatocin kasashen ketare za su kiyaye ikon mallakar ilmi na kasar Sin. Kasar Sin za ta ci gaba da inganta shawarwari da kanana da matsakaitan kamfanonin kasar Sin, da kamfanoni masu zaman kansu, da kamfanoni masu jarin waje, domin kiyaye ikonsu yadda ya kamata, da samar da yanayi mai kyau wajen gudanar da harkokin sabbin fasahohi da na kasuwanci."

Game da yadda za a aiwatar da wannan aiki kuma, an ce, a halin yanzu, kasar Sin ta riga ta kafa tsarin dokoki na kare ikon mallakar ilmi da matakai masu tsanani, kana, tana mai da hankali sosai kan kiyaye ikon mallakar ilmi na kasashe masu ci gaba, da na kasashe masu tasowa a fannonin da suke da kwarewa, lamarin da ya sami amincewa daga gamayyar kasa da kasa, ya kuma ba da gudummawa wajen raya ayyukan samar da sabbin fasahohi, da kyautata yanayin cinikin kasar Sin.

Kana, bisa rahoton Alkaluman kirkire kirkire na kasa da kasa na shekarar 2019 ko GII a takaice, wanda kungiyar ikon mallakar ilmi ta kasa da kasa ta fidda, an ce, an daga matsayin kasar Sin zuwa 14 cikin kasa da kasa, wadda ta kasance gaba cikin kasashe masu samun matsakacin kudin shiga. Haka zalika kuma, kasar Sin tana kan matsayi na 31 cikin kasa da kasa, cikin rahoton Yanayin gudanarwar harkokin kasuwanci na shekarar 2020 da bankin duniya ya fidda.

Bugu da kari, ana mai da hankali sosai kan sabuwar bukata ta "karfafa aikin ba da taimako ga wadanda suke neman kare ikon mallakar ilmi a kasashen ketare", wadda aka fidda cikin sabon shawarwarin inganta ayyukan kare ikon mallakar ilmi. Matakan da za a dauka sun hada da kyautata tsarin yin rigakafin kan sabanin ikon mallakar ilmi a kasashen ketare, da kara yin nazari da kuma bincike kan babbar karar da aka gabatar, da kafa tsarin bin labarai na gyaran dokokin ikon mallakar ilmi na kasashen ketare, da samar da labaran yin rigakafi kan kalubalolin dake gabanmu cikin lokaci, da ba da taimako kan yadda za a fuskanci sabanin ikon mallakar ilmi a kasashen ketare, da kafa tsarin warware sabanin ikon mallakar ilmi a kasashen waje da dai sauransu. Ta yadda za a iya kare ikon mallakar ilmi na 'yan kasar Sin a kasashen ketare yadda ya kamata.

Dangane da wannan batu, mataimakin shugaban hukumar ikon mallakar ilmi na kasar Sin Gan Shaoning ya bayyana cewa, "Karfafa aikinmu na kafa dandalin kare ikon mallakar ilmi, zai kara karfin kiyaye ikon mallakar ilmi na al'ummar Sin a kasashen waje. Ya kamata mu gaggauta aikin yin mu'amala kan harkokin kare ikon mallakar ilmi da kasashen waje, da kyautata dandalin samar da labarai game da harkokin kiyaye ikon mallakar ilmi a kasashen ketare, da kafa cibiyar warware sabanin ikon mallakar ilmi ta kasar Sin a kasashen ketare, wadannan matakai za su ba da taimako matuka ga kamfanonin Sin, wajen aiwatar da ayyukansu a kasashen ketare."

Haka zalika kuma, sabbin shawarwarin da aka fidda sun nuna bukatar ci gaba da kyautata tsarin kare ikon mallakar ilmi, ta hanyoyin dokoki, siyasa, tattalin arziki da kuma fasahohi da sauransu, domin karfafa dabaru ta fuskar kiyaye ikon mallakar ilmi. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China