Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar 'yan sama jannatin Chang'e-4 na kasar Sin ta karbi lambar karramawa daga kungiyar RAeS ta Birtaniya
2019-11-26 11:25:35        cri
A jiya Litinin ne tawagar 'yan sama jannati da suka yi aikin bincike ta kumbon Chang'e-4 na kasar Sin, ta karbi lambar karramawa ta ma'aikata masu hazaka daga kungiyar RAeS ta Birtaniya. An gabatar da lambar karramawar ne yayin taron shekara shekara na kungiyar ta Royal Aeronautical Society, wanda ya gudana a birnin London.

Wannan lamba ta karramawa da tawagar 'yan sama jannatin ta karba karkashin jagorancin shugabanta Wu Weiren, wanda ya jagoranci aikin tsarawa da harba kumbon binciken na kasar Sin, ita ce irinta ta farko da kungiyar RAeS ta taba bayarwa ga wata tawagar kasar Sin, tun kafuwarta shekaru 150 da suka gabata.

Bayan bikin karbar lambar karramawar, Mr. Wu ya jinjinawa RAeS, da ma kwamitin ba da lambar karramawar, yana mai fatan sauran kasashen duniya da kungiyoyi, za su yi hadin gwiwa da Sin a fagen gudanar da binciken kimiyyar sararin samaniya, ta yadda daukacin bil Adama zai amfana.

Kumbon bincike na Chang'e-4 mallakar kasar Sin, ya kafa tarihi na kasancewa kumbo na farko da ya taba sauka a gefen wata mafi nisa, a ranar 3 ga watan Janairun shekarar nan ta 2019. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China