Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na goyon bayan aiwatar da gyare-gyare a kwamitin Sulhu na MDD
2019-11-26 10:15:15        cri
Wakilin kasar Sin a MDD, ya ce kasarsa na goyon bayan aiwatar da gyare gyaren da suka dace a tsarin kwamitin sulhu na MDD domin biyan bukatun da ake da su a yanzu.

Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ne ya bayyana haka yayin zama na 33 na babban zauren majalisar na 74 kan "daidaito ta fuskar wakilci da kara mambobin kwamitin sulhu da sauran batutuwan da suka shafi kwamitin".

Ya ce ya kamata a bada muhimmanci ga batun kara wakilci da kuma sauraron kasashe masu tasowa, musammam na Afrika.

Wakilin na kasar Sin ya kara da cewa, dole ne gyare-gyaren ya kara damarmakin samun kujeru a kwamitin ga kanana da matsakaitan kasashe da kuma shiga a dama da su cikin harkokin da ya shafe su. Yana mai cewa wannan ita ce hanya daya tilo ta tabbatar da tsarin demokradiyya da gaskiya da ingancin kwamitin.

Zhang Jun ya kuma bayyana cewa, huldar kasa da kasa na fuskantar kalubale, kuma ita ake matukar bukata ga hadin kan majalisar. Ya ce aiwatar da gyare-gyaren ya shafi muhimman muradun mambobi da makomar majalisar, kana zai kai ga samar da gagarumin gyara ga tsarin shugabanci a duniya da odar kasa da kasa.

Har ila yau, ya ce ana bukatar tattaunawa mai zurfi da kuma tuntuba ta fuskar demokradiyya domin samun mafita mai inganci da za ta kunshi dukkan muradu da damuwar dukkan bangarori, da cimma matsaya guda, tare da samun goyon bayan dukkan kasashe mambobin majalisar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China