Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin MDD ya isa Yemen a kokarin kawo karshen yakin basasar kasar
2019-11-25 10:16:54        cri

A jiya Lahadi manzon musamman na MDD Martin Griffiths ya isa Sanaa, babban birnin kasar Yemen a yayin da aka fara ganin alamun bangarorin dake rikici da juna a kasar na kawo karshen yakin basasar da ya tagayyara kasar.

A cewar wasu jami'an mayakan 'yan tawayen Houthi, Martin Griffiths ya tsayar da lokacin da zai gana da shugabannin 'yan tawayen Houthi.

Ziyarar ta zo ne kwanaki biyu bayan da Griffiths ya yiwa kwamitin sulhun MDD bayani, inda ya ya yi tsokaci game da irin ci gaban da aka samu game tattauna batun rikicin siyasar Yemen da kawo karshen yakin basasar kasar.

Ya fadawa kwamitin sulhun MDD a ranar Juma'a cewa, ci gaban da aka samu zai taimakawa kokarin da ake na magance tashin hankalin Yemen ta hanyar matakan siyasa, inda ya kafa hujja da yarjejeniyoyin Riyadh da Stockholm, wadanda aka cimma matsaya kan su a ranar 5 ga watan Nuwambar wannan shekarar da kuma watan Disambar bara.

Wata alamar ci gaban da mista Griffiths ya bayyana cikin jawabin nasa shi ne, an samu raguwar kusan kashi 80% na hare hare ta jiragen sama a duk fadin kasar cikin makonni biyun da suka wuce.

Jami'in MDDr ya ce wadannan wasu alamu ne dake nuna cewa an samu gagarumin ci gaba wanda zai taimaka wajen gina tubalin kawo karshen yakin basasar Yemen wanda aka shafe sama da shekaru hudu ana fuskanta a kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China