Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya gana da tsohon firaministan Japan
2019-11-25 09:52:32        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, a ranar Lahadi ya gana da tsohon firayim ministan kasar Japan Yasuo Fukuda, game da batun kyautata dangantakar kasashen biyu.

Yayin tattaunawar, Wang ya ce, a halin yanzu dangantakar dake tsakanin Sin da Japan tana ci gaba da kyautatuwa, kuma ya kamata bangarorin biyu su hada hannu wajen karfafa fahimtar juna da amincewar siyasa a tsakaninsu, da zurfafa hadin gwiwa, da zurfafa mu'amala tsakanin mutum da mutum da musayar al'adu kuma su kawar da duk wani sabani domin samun kyakkyawan ci gaban dangantakar dake tsakaninsu.

Ya kamata bangarorin biyu su karfafawa al'ummomin kasashen biyu gwiwa wajen kyautata mu'amala, da inganta yanayin fahimtar juna kuma su mayar da batutuwan da za su karfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Japan gaba tun daga tushe, in ji mista Wang.

Ya ce lokaci ya yi da ya kamata Fukuda ya jagoranci kafa wata cibiyar musayar al'adu don kyautata makomar al'ummar Asiya, wanda kasar Sin za ta ba da cikakken goyon bayanta.

A nasa bangaren, Fukuda ya ce, a halin yanzu dangantakar dake tsakanin Japan da Sin yana samun tagomashi matuka.

Fukuda ya ce, ya tattaro mutane masu hangen nesa daga dukkan fannonin rayuwa na kasar Japan domin kafa wata cibiyar musayar al'adun al'ummar Asiya, da nufin kyautata mu'amala tsakanin mutum da mutum da kuma musayar al'adu tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a bayar da kyakkyawar gudunmowa wajen gina al'ummar Asiya tare kuma da samar da makoma mai haske ga dukkan bil adama.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China