Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Yadda kasar Amurka ke tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin zai haifar mata da matsala
2019-11-24 20:18:45        cri

A kwanakin baya, majalisun kasar Amurka suka zartas da shirin doka mai alaka da yanayin hakkin dan Adam da tsarin dimokuradiya a yankin Hong Kong na shekarar 2019, inda take fakewa da sunan dimokuradiya da 'yancin dan adam, don neman tsoma baki cikin harkokin Hong Kong, da suka kasance harkokin cikin gidan kasar Sin, lamarin da ya sabawa dokokin kasa da kasa, gami da wasu manyan ka'idojin da ake bi wajen hulda da sauran kasashe. Hakan ya ba mutanen duniya damar fahimtar manufar kasar Amurka na mulkin danniya, da nuna isa a fannin siyasa. Tabbas zai sa gamayyar kasa da kasa kyamar matakan kasar Amurka na rashin adalci, wadanda suka keta dokokin kasa da kasa.

Bari mu duba shirin doka na banza da majalisun kasar Amurka suka gabatar. Wannan shirin doka ya bukaci gwamnatin kasar Amurka da ta tantance yanayin da yankin Hong Kong na kasar Sin ke ciki, a fannonin "Cin gashin kai", da "Dimokuradiya", da kuma "Hakkin dan Adam", a kowace shekara. Sa'an nan gwamnatin za ta yanke shawara kan ko za ta daina baiwa Hong Kong tukwici a fannin ciniki, da saka takunkumi kan wasu jami'ai da kamfanoni na yankin Hong Kong. Matakin da majalisun kasar Amurka suka dauka ya zama dora dokar gida a kan dokokin kasa da kasa, lamarin da ya nuna yadda wasu 'yan siyasa na kasar Amurka suke da girman kai matuka. Sai dai jama'ar kasar Sin sam ba za su yarda da wannan mataki na rashin adalci ba.

Duniyarmu na cikin wani zamani na neman zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki. Sa'a nan wasu manyan manufofin cikin dokokin kasa da kasa, irinsu zama daidai wa daida tsakanin kasashe daban daban, da rashin tsoma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe, sun riga sun shiga zukatan jama'ar kasashe daban daban, ta yadda suka zama wasu ginshikan manufofin da kowa ya yarda. Hakika duk wani matakin rashin adalci da aka dauka a kasar Amurka ya kan bata kimar kasar, da dora kasar kan hanyar lalacewa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China