Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta taimaki kasashen Afirka don samun ci gaba
2019-11-23 17:11:36        cri
Yau Asabar, memban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 a birnin Nagoya na kasar Japan.

Wang ya bayyana cewa, kasar Sin na nuna kwazo wajen tallafawa Afirka ficewa daga "tarkon rashin samun ci gaba". Ya ce a halin yanzu karancin kudade shi ne kalubale mafi girma ga ci gaban kasashen Afirka, kuma ana rashin jarin da yawansu ya kai dala biliyan 100 a bangaren gina muhimman ababen more rayuwar al'umma a nahiyar a kowace shekara. Haka kuma muhimman ayyukan da kasar Sin ke kokarin ginawa a Afirka na haifar da moriya ta dala biliyan 50 ko fiye a kowace shekara a nahiyar. Alal misali, layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi ya samar da guraban ayyukan yi kusan dubu 50 a yankin a kowace shekara, abun da ya taimaka ga ci gaban tattalin arzikin Kenya da kaso 1.5 bisa dari.

Ya ce hadin-gwiwa tsakanin kasashen dake tasowa, taimako ne da suke baiwa juna. Kasar Sin na maida hankali sosai kan batun bashi, da taimakawa kasashen Afirka inganta kwarewa a fannin daidaita basussuka. Har wa yau, an samu nasarori masu dimbin yawa wajen raya ayyukan da suka shafi "ziri daya da hanya daya" tsakanin Sin da Afirka, kuma shawarar "ziri daya da hanya daya" na tafiya daidai da ajandar neman ci gaba mai dorewa ta shekara ta 2030, da ajandar ci gaba ta shekara ta 2063 ta AU gami da manufofin samun ci gaba na kasashen Afirka daban-daban, abun da zai taimaka sosai ga neman ci gaba tsakanin Sin da Afirka.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China