Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin: Ya dace Sin da Rasha su kiyaye adalcin kasa da kasa
2019-11-22 20:27:06        cri

A yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, a yanzu ya dace kasashen Sin da Rasha su yi kokari tare, domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, da adalci a fadin duniya.

Kwanan baya shugaban Rasha Putin, ya halarci dandalin tattaunawa kan zuba jari karo na 11, mai taken "Rasha tana kira", inda ya bayyana cewa, Amurka tana kokarin hana ci gaban Sin da Rasha, kuma wannan mataki kuskure ne da ta dauka.

Kan wannan, Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin ta jinjinawa kalaman shugaba Putin. Ya ce yanzu haka wasu kasashe suna aiwatar da manufar bangaranci, har ma suna tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashe, tare kuma da daukar matakan saka takunkumi, duk wadannan matakai kuwa, na gurgunta tsarin kasa da kasa, kuma ko shakka babu, ba su samu amincewa daga al'ummun kasashen duniya ba. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China